Gwamnatin jihar Kwara ta rushe katafaren ginin wani jigon jami'iyyar APC

Rushe katafaren shagon saide-saide na Crystal Place da ke Ilorin mallakin tsohon dan majalisar wakilai Moshood Mustapha ya tayar da kura a jihar Kwara.

Wannan mataki ya nuna karara irin rashin jituwa da ke tsakanin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da Mustapha Moshood wadanda 'yan jam’iyya daya ne a jihar.

An yi zargin an rushe ginin ne a daren Lahadi tare da ‘yan sanda su na ba da tsaro kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Mai wurin ya yi zargin cewa an bashi sanarwar tashi a kurarren lokaci. Amma dai hukumar kula da tsara birane ta jihar Kwara ta hannun Sulaiman Abdulkareem ta ce tun farko an ba Mustapha filin ne domin ya gina tashar mota. Amma kawai ya yi gini mai tsawo na katafaren shago da hakan ke nuna kauce wa tsarin gwamnati na amfani da kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp