Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga na sa'o'i 18


Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf




Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga na tsawon sa'o'i 18 daga karfe 12:00 na dare zuwa karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar.


Daily Trust ta rawaito cewa hakan ya biyo bayan tuntubar da hukumomin tsaro suka yi a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Baba Halilu Dantiye ya fitar a ranar Juma’a.


Dantiye ya bukaci al'umma da su mutunta umurnin na takaita zirga-zirga tare da ba da gudummawar su wajen tabbatar da hakan, ya ce aniyarsu shi ne gudanar da zabe cikin gaskiya,kuma cikin lumana.


A cewar sa matakin ya shafi mutane da ababen hawa a fadin kananan hukumomi 44 LGA da kuma maza bu 484 na jihar.


Dokar ta zo ne da sa'o'i 24 gabanin zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa ranar Asabar, 26 ga Oktoba.


Sanarwar ta ce an tsara matakin ne domin tabbatar da tsaro, da hana duk wani abu da zai iya kawo cikas, da kuma samar da yanayi mai kyau na gudanar da sahihin zabe.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp