Gwamnan jihar Borno/Baba Gama Umarar Zulum |
Kwamishinan Lafiya da ayyukan al'umma,na jihar Farfesa Baba Gana ya bayyana hakan a cibiyar kula da ido da ke Maiduguri, ya ce daga cikin samfura dari biyu da aka aika domin yin gwaji, goma sha bakwai sun kamu.
A cewarsa bullar cutar ta samo asali ne sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi kwanakin baya a sassan jihar.
Farfesan ya ce wuraren da aka samu bullar cutar sun hada da Jere, Mafa, Konduga da kuma Dikwa.
A cewar sa haryanzu ba a samu rahoton mace-mace ba, kwamishinan ya ce ana samun karuwar masu kamuwa da cutar kwalarar a kananan hukumomin da dama, musamman ma a lokacin da jihohin Adamawa da Yobe da ke makwabtaka da ita cutar ta bulla.
Ya ce an samu rahoton mutum 451 da ake zargin sun fito ne daga kananan hukumomi daban-daban amma 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar.
Don haka gwamnatin jihar ta ba da sanarwar daukar matakin gaggawa don shawo kan barkewar cutar, yayin da hukumomin jin kai kamar hukumar lafiya ta Duniya WHO da Médecins Sans Frontières MSF suka samar da kayayyakin shawo kan matsalar, kuma an samar da alluran rigakafi kusan 400,000.