Gwamna Zulum na jihar Borno na neman majalisa ta sahale masa karin N61b a kasafin kudin cike gibi na shekarar 2024

Babagana Umara Zulum


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bukaci majalisar dokokin jihar da ta sahale masa karin biliyan 61 akan kasafin farko kudin na N358.7b na shekarar 2024,domin cike gibi da gudanar da wasu ayyuka.


Kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulkarim Lawan ne ya karanta wasikar gwamnan a zauren majalisar a yau


Ƙarin kasafin kudin dai zai shafi muhimman ayyuka da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a ranar 10 ga watan Satumba, wadda ta shafi kusan mutane miliyan 2 tare da lalata wasu sassan Maiduguri da ƙananan hukumomin da ke kewaye da ita.


Kasafin zai kuma kunshi kudaden da  gwamnati ke kashewa wajen bayar da agajin gaggawa, tallafawa manoma, farfado da tattalin arziki da kuma kula da muhalli.


A ranar Alhamis ne Gwamna Zulum ya zagaya domin tantance wurare, hanyoyi,da asibitocin da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan domin tantance su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp