A Larabar nan ne ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli Farfesa Joseph Terlumun Utsev ya kaddamar da wani kwamitin kwararru da zai samar da dabarun daƙile afkuwar ambaliyar ruwa a fadin kasar nan.
Kwamitin zai yi aikin samar da taswirar inganta madatsun ruwa da tsarin zamantakewa da ma wasu karin shirye-shiryen inganta muhalli cikin gaggawa.
Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu muhimman tsare-tsare guda biyu da suka haɗa da kafa asusun bayar da agajin Ibtila'i da samar da kwamitin yaki da ambaliya ruwa .
Wadanda suka halarci taron Kaddamar da kwamitin sun hada da
Ministan Watsa Labarai, Muhammad idris da na Kasafin Kudi sanata Abubakar Atiku Bagudu, da minista Muhalli Balarabe Abbas inda dukansu suka jaddada bukatar ganin Kwamitin ya fara aiki nan take.
Kazalika gwamatin Shugaba Tinubu ta ware kudaden tallafin yaki da Ibtila'in ambaliyar ga ilahirin jihohin kasar
Wannan matakin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen shawo kan iftila'in ambaliyar ruwa da samar da kariya ta dindindin.