Dole mu hadu mu gyara Nijeriya, idan ba haka ba za ta durkushe - Shugaba Tinubu

 Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bayyana cewa dole ne kasar ta sake gyara don samun ci gaba da wadata ko kuma ta koma 'yar gidan jiya da hakan na iya durkusar da ita.


Sai dai, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa bayan da ta karbi ragamar shugabancin kasar watanni 16 da suka gabata, ta yanke shawarar sake fasalin tattalin arziki a siyasance da tsare-tsaren tsaro, duba da irin mawuyacin halin da kasar nan ta samu kanta.


Ya koka da yadda kasar ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali saboda rashin damarmaki da kura-kurai a baya, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da kada su bari kura-kuran da aka gudanar a baya su cigaba da bin kasar nan a gaba.


Wannan wani bangare ne na jawabin da shugaban kasar ya gabatar a kasar, a yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun 'yancin kai, wanda aka gabatar a safiyar ranar Talatar nan.


Nijeriya ta samu 'yancin kanta daga Birtaniya a ranar 1 ga Oktob


a, 1960.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp