Shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPCL Mele Kyari ya ce cire tallafin mai ya taimaka wurin rage fasakaurin sa ta kan iyakokin kasar.
kyari ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels Lahadin, inda ya bayyana cewa tallafin ya haifar da rashin tazara mai yawa na farashi a tsakanin Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita, lamarin da ya sa fasakwauri ya ragu sosai.
Ya bayyana cewa shekaru da dama, tallafin ya samar da dama ga masu fasa-kwaurin.
Kafin cire tallafin, Kyrari ya jaddada bambancin farashin yana da yawa, abin da a cewar sa shi ke ƙarfafa masu yin fasa kwaurin.