CBN ya musanta batun daina karbar tsoffin takardun kudi na Naira a watan Disamba mai zuwa

Sai dai bankin ta hannun mukaddashin daraktan sadarwa Sidi Ali Hakama, ya shawarci 'yan Nijeriya da su rungumi tsarin hada-hadar kudi na zamani.

Akwai dai wani labari da ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta, ana tsoratar da mutane cewa daga ranar 31 GA watan Disamba mai zuwa, za a daina karbar tsoffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000.

Idan za a iya tunawa dai, bankin na CBN ya sanar da a cigaba da amfani da tsoffin takardun kudin hade da sabbin kamar yadda kotun koli ta umurta bayan karar da aka shigar a watan Nuwambar 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp