Mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga ya kawar da yiwuwar dawo da tsohuwar ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i, Betta Edu cikin jerin ministoci shugaba Bola Tinubu.
Onanuga ya ce Tsohuwar ministar Betta edu ba za ta sake samun dama ba a gwamnatin shugaba Tinubu, ta tafi kenan.
An dakatar da Edu ne a ranar 8 ga watan Janairun shekarar nan biyo bayan wani zargin badakalar wasu kudade a ma'aikatar da take jagoranci.