Babban sufeton 'yansandan Nijeriya ya ba da umurnin bude sakatariyar kananan hukumomin jihar Ribas

IGP Kyaode Egbetokun


Babban sufeton 'yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin bude sakatariyar kananan hukumomin jihar Ribas bayan rantsar da shugabannin sabbin shugabannin kananan hukumomin.


Kwamishinan ‘yan sandan da aka tura, CP Mustapha Bala bisa umarnin IGP, Kayode Egbetokun ya ba da umarnin a gaggauta janye dukkan jami’an ‘yan sandan da aka tura domin rufe sakatariyar kananan hukumomin.


Lamarin ya faru ne bayan gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar.


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe Koko, ta tabbatar da hakan a safiyar Litinin dinnan.


An rufe sakatariyar kananan hukumomin ne a watan Yuni sakamakon rashin jituwar da ta barke tsakanin shugabanin riko na kananan hukumomin a wancan lokacin da ke biyayya ga gwamna Siminalayi Fubara da kuma sauran da ke biyayya ga ministan tarayyar Abuja Nyesom Wike.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp