Ba na tsoron mutuwa, amma zan iya rungumar sulhu - Bello Turji

 


Ba na tsoron mutuwa, amma idan gwamnati na so a sasanta, zan ajiye makamaina na rungumi sulhu, in ji rikakken dan bindiga Bello Turji da ya addabi wani sashe na arewa maso Yammacin Nijeriya, musamman Sokoto, Zamfara da Katsina.


Bello Turji da yake cikin jerin mutane 43 da hedikwatar tsaron Nijeriya ke nema ruwa jallo, ya yi wannan furucin ne a cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna biyar da dakika 40 da jaridar Daily Trust ta nazarta.


A cikin faifan bidiyon, Bello ya na fada wa jami'an tsaro cewa yanzu haka ya shirya mutuwa, sai dai ya roki gwamnatin jihar Zamfara da ta tarayya da su zo a zauna domin lalubo bakin zaren matsalar a sulhunta mutane su zauna lafiya.


Bello Turji ya tabbatar da mutuwar ubangidansa Halilu Sububu, inda ya bugi kirjin cewa wannan kisa da jami'an tsaro suka yi wa Kachallah Buzu, ba zai sare masa guiwa ba.


Sai dai ya kara da cewa a shirye yake ya ajiye makamansa muddin gwamnati ta yarda ta saurare shi don a yi sulhu kowa ya huta.


Ya bayyana cewa shi fa ba ya zo duniyar nan bane don ya zauna, a kodayaushe shirye yake da ya bar duniyar da ba ta da tabbas.


A cikin faifan bidiyon Bello Turji, ya yi ikirarin cewa ba wannan lokacin aka fara kashe-kashen jama'a ba. Ya kara da cewa idan al'ummar jihar Zamfara sun daina kashe musu mutane, to su ma za su daina kashe al'umma.

1 Comments

  1. Mu abinda mukadau keka abokin ai kin gwamnatin zalinci bello turji Wanda duk akaba ai ki irin naka Kuma yayi kuskure irin naka ya amsa to koyayi nasara ko baiyiba tozasuka shekane saboda kamu da sirin dasirin da akayi dakai

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp