![]() |
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf |
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ba gudu ba ja da baya za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar Asabar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mika tutocin takara na jam’iyyar NNPP ga ‘yan takarar shugabanin kananan hukumomin jihar 44 da kansiloli a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, ya ce da taron wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a ranar Alhamis ya samu halartar manya-manyan mabiya da magoya bayan jam’iyyar.
A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Simon Ameboda ta rushe shugabanni da mambobin hukumar zaben jihar KANSIEC tare da dakatar da gudanar da zaben har sai an gyara hukumar yadda ya kamata.
Gwamnan, ya ce a halin yanzu jihar ba za ta bari wasu suzo su dagula zaman lafiyar da ‘yan kasa ke samu ba, ya kara da cewa gwamnatin jihar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar KANSIEC na da dukkan goyon bayan da tsarin mulki ya ba shi wajen gudanar da zaben.