Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa rashin bin ka’ida da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi sune suka haddasa tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.
Atiku na mayar da martani ne kan karin farashin man fetur da kamfanin NNPC ya yi, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.
Atiku ya zargi shugaba Tinubu da kauda kai ga ‘yan Nijeriya kamar yadda jaridar Punch ta ruwairo.
Kamfanin NNPC ya kara farashin man fetur daga N897 kan kowace lita zuwa N1,030 a Abuja.