Asusun ba da lamunin karatu na kasa ya ce ya raba Naira biliyan 10 ga dalibai 40,000 a Nijeriya

Asusun ba da lamunin karatu



Asusun ba da lamunin karatu ta Nijeriya ya ce, zuwa yanzu an raba kimanin Naira biliyan 10 ga dalibai 40,000 tun bayan fara shirin bayar da bashun ga dalibai.



 Manajan daraktan hukumar bayar da lamunin karatun NELFUND Akintunde Sawyerr ya bayyana haka a gidan talabijin na Channels cikin Shirin  Politics Today, a ranar Talata.


Ya ce kimanin dalibai 370,000 ne suka yi rajista a asusun bayar da lamunin karatu, yayin da dubu 280,000 ba su samu nasarar shiga tsarin ba.



Ya ce kusan dubu 40,000 daga cikinsu an sun samu nassara kuma duk an biyasu kudaden.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp