Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da kama wani Mai Unguwa Usamatu Adamu daga kauyen Runka da ake zargi da hada baki da barayin daji don aikata ba daidai ba a jihar.
A cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sandan Sadiq Aliyu Abubakar ta ce an kama Mai Unguwar mai kimanin shekaru 45 a kauyen Sabon Gida a karamar hukumar Igani ta jihar Kaduna bayan da jami'an tsaro suka bibiye shi.
Sanarwar 'yan sandan ta ce an kama Mai Unguwar ne bayan da jami'an tsaro suka samu bayanan sirri da ke zarginsa da hannu a satar mutane a yankin Runka ta karamar hukumar Safana jihar Katsina.
Sadiq Aliyu Abubakar ya sanar cewa wanda Ake zargin ya amsa laifinsa, har ma ya lissafto Rabe Sada da aka fi sani da BBC da Nasiru Shu'aibu a matsayin masu taimaka masa dukkaninsu daga garin nan Runka.