Kungiyar kula da babban birnin tarayya Abuja ta ce ta kama wani dan kwangilar da ya ke lalata fitilun tituna a yankin.
Shugaban kungiyar ta (AMMC), Mista Felix Obuah, ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan duba wasu gyare-gyare fitilun kan titi.
Koda yake bai ambaci sunan dan kasar waje ba, shugaban kungiyar ya ce kamfanin da dan kwangilar ke aiki sananne ne, inda ya kara da cewa wanda ake zargin zai girbi abunda ya shuka
A cewarsa, dan kwangilar ya shiga cikin masu lalata fitilun tituna domin samun damar yin kwangilar.
Obuah ya ce, "mafi yawan lokuta muna tunanin miyagun batagari ne ke da hannu wajen lalata fitilun tituna, sai a yau mu ka gano cewa manyan ’yan kwangila ne ke da hannu wajen yin zagon kasa ga kyakkyawan kokarin minista da kungiyar ta (AMMC)