'Yan sanda a jihar Lagos sun kama wani malamin makaranta Gbolahan Osinusi, mai shekaru 42 bisa zargin keta haddin wata dalibarsa. Daily Trust ta ce malamin ya kwashe shekaru 5 cur yana alaka da wannan daliba tun tana 'yar shekara 12 a duniya. Kazalika, an zargi Gbolahan da tursasa mata ta zubar da juna biyun da ya dirka mata a tsawon wannan lokacin.
Ana zargin malamin da ke koyarwa a makarantar Ketu-Epe da kuma tursasa wa dalibar yin rantsuwa da Allah cewa ba za ta fada wa kowa ba halin da ake ciki.