A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sanata Bashir Lado, ta ce yanzu za a tantance sabbin ministocin ne a ranar Laraba, maimakon Talatar da a baya aka ayyana.
Sanarwar ta ce an dauki wannan matakin ne domin ba mutanen damar gabatar da dukkanin bayanan da ake bukata kafin tantancewa.
Sanarwar ta ce za a fara tantance su da misalin karfe 12 na rana.