Kungiyar gamayyar kungiyoyin jami'iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya sun ba shugaban jami'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje wa'adin kwanaki 7 na ya yi murabus daga mukaminsa cikin ruwan sanyi.
Shugaban kungiyar Hon Saleh Abdullahi Zazzaga a taron manema labarai a Jos babban birnin jihar Plateau, ya ce idan wa'adin ya kare Ganduje bai sauka, da yiwuwar ya dauki matakin shari'a a kansa.
Wannan wa'adi dai na karewa a ranar Litinin 14 ga watan Oktoba, 2024.
Saleh Zazzaga dai na kalubalantar cewa a babban taron jami'iyyar da ya gudana a ranar 26 ga watan Maris, 2022, an ba yankin Arewa ta tsakiya damar samar da shugaban jami'iyyar APC na kasa.
Bayan murabus din Abdullahi Adamu wanda ya fito jihar Nasarawa, maimakon a mayar da kujerar a yankin, sai aka ba Ganduje wanda ya fito daga yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, wanda a cewarsa hakan ya saba wa kundin tsarin jami'iyyar.