A yau ne za a fara shari'ar masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja, Kano, Kaduna da Borno, kamar yadda mataimakin babban sufeton 'yan sanda Dasuki Galadanchi ya bayyana.
Galadanchi ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya da aka kammala a Abuja.
Ya ce wadanda za a gurfanar gaban kotun su 126 ne da aka zargin su da laifin daga tutar kasar Rasha tare da neman a sauya tsarin mulki a lokacin zanga-zangar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane tare da sace dukiyoyin jama’a da na gwamnati a wasu jihohin kasar.
Lauyan mai kare hakkin bil’adama Femi Falana ne zai jagoranci sauran lauyoyin da za su kare masu zanga-zangar a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja.