Za mu daukaka kara don neman a cire Ganduje daga shugabancin APC - 'Yan Arewa ta Tsakiyar Nijeriya


Gamayyar kungiyoyin jami'iyyar APC na yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya sun ce ba za su bari Abdullahi Umar Ganduje ya kawo rudani da rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yan Jami'iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiya ba.

Haka kuma gamayyar kungiyar ta ce ba za ta yi kasa a guiwa ba, sai ta daukaka kara don neman hakkin gurbin shugabancin jami'iyyar APC da yake hakkin yankin a tsarin jami'iyyar.

Hakan ya biyo bayan korar karar da kotun tarayya ta yi da kr neman a cire Ganduje daga matsayin Shugaban jami'iyyar APC na kasa a mayar da gurbin a yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya bayan da Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa ya yi murabus.

Da yake zantawa da DCL Hausa ta wayar tarho daga Jos babban birnin jihar Plateau, shugaban kungiyar Saleh Abdullahi Zazzaga, ya ce za su bi dukkanin hanyoyin da doka ta gindaya don neman hakkinsu na dawo da shugabancin APC a yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya.

A baya dai, wannan kungiya ta maka jami'iyyar APC da Abdullahi Umar Ganduje da hukumar zaben INEC a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda take bukatar da kotu ta soke nadin da aka yi wa Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Shugaban jami'iyyar APC na kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp