Za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa in ji Shugaba Tinubu

Za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa in ji Shugaba Tinubu 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbacin za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano don inganta harkar sufuri a Nijeriya da yammacin Afirka baki daya.


Tinubu ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai hedkwatar kamfanin gina layin dogo na kasar Sin (CRCC) a birnin Beijing, mai magana da yawun sa Ajuri Ngelale, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.


Shugaban ya amince da rawar da kamfanin ke takawa a matsayin amintaccen abokin huldar gwamnatin tarayya a cikin shirin samar da ababen more rayuwa ga 'yan Nijeriya, ya kuma yaba da ayyukan da yake yi na layin dogo a Nijeriya.


Yace yana da matukar muhimmanci ya baiwa al’ummar Nijeriya tabbacin cewa a duk fadin kasar, za a kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano, da kuma yin yadda zai inganta sufuri a Nijeriya da yammacin Afrika baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post