‘Yan sanda sun kama wasu mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Kaduna, tare da kwato bindigogi da harsasai

 ‘Yan sanda sun kama wasu mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Kaduna, tare da kwato bindigogi da harsasai



Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane 11 da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da kwato tarin makamai da makudan kudade.


A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, Mataimakin Sufeto Mansir Hassan, ya ce kamen na da nasaba da sace wani hakimi a ranar 14 ga watan Agustan 2024, wanda aka sake shi bayan kwanaki biyu.


Hassan ya kara da cewa, jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar 'yan sakai sun kai sumame kauyuka uku da ke karamar hukumar Lere, inda suka kama wasu mutane biyar tare da kwato wata bindiga kirar ganga guda, mota, babur, da kuma wayoyin hannu da dama.


A wani samame na daban kuma an kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a wani wurin ajiye motoci, lamarin da ya kai ga kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu, da wasu manyan bindigogin guda biyu, da wasu makudan kudade.


Sanarwar ta ci gaba da cewa,dangane da yin garkuwa da wani hakimi a ranar 14 ga watan Agusta, 2024, wanda aka sako a ranar 16 ga watan Agustan 2024, jami’an ‘yan sanda a Saminaka tare da hadin gwiwar 'yan sakai sun kai farmaki kauyuka uku a karamar hukumar Lere, wato Maraban Wasa Gurzan Hakimi Mariri.


An kama wadanda ake zargi guda biyar Abdulhamid Abubakar (mai suna Bala, mai shekaru 30), Danjuma Luka (wanda aka fi sani da Uba, 25), Ayuba Simon (50), da Idi Saleh (57). Kayayyakin da aka gano sun hada da bindiga guda daya, koriyar mota kirar Golf, babur Bajaj, da wayoyin hannu guda takwas.

Post a Comment

Previous Post Next Post