‘Yan Nijeriya masu shaidar dan kasa ta NIN ne kadai za su iya sayen shinkafar da gwamnatin tarayya za ta sayar a ₦40,000 – Ministan Noma
Gwamnatin tarayya ta ce wadanda ke da rajistar shaidar dan kasa ta (NIN) ne kadai za su samu damar sayen shinkafar da gwamnatin za ta sayar a naira 40,000 kan ko wane buhu.
Shugaba Bola Tinubu wanda ya samu wakilcin ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin dakile tsadar kayan abinci a kasuwannin Nijeriya.
Kyari ya kara da cewa za a sayar da su a hannu ne kawai kuma namiji ko mace kowa zai iya mallakar buhu daya.
Ya ce shinkafar wacce za a sayar da ita kan kudi Naira 40,000 a kan kowane 50kg,gwamnatin tarayya ce ta sa baki wajen sayar da shinkafar don magance matsalar abinci da ake fama da ita a Nijeriya.
A cewarsa tallafin abincin ya dace a wannan lokacin idan aka yi la’akari da lokuta da kalubalen da ake ciki a wannan kasa mai girma.