'Yan Nijeriya 400 da Dubai ta dawo dasu sun sauka a Abuja

'Yan Nijeriya 400 da Dubai ta dawo dasu sun sauka a Abuja

An dawo da ‘yan Nijeriya dari hudu daga hadaddiyar daular Larabawa Dubai, inda suka iso Nijeriya, kamar yadda wani rahoto da gidan talabijin na Nijeriya ya fitar.


Jami’an ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure da kuma hukumar hana safar mutane ta kasa ne suka tarbi mutanen a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.


Wa'yanda aka maido dasu dari hudu da suka hada da mata 90 da maza 310 daga Dubai din sun shiga kasar ne da zummar karatu daga bisani suka bige da kwadago ba tare da takar da ba.


Idan za a iya tunawa,ko a kwanakin baya gwamnatin tarayya ta dawo da ‘yan Nijeriya 190 daga Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Yulin 2024.


A watan Yuni, bayan tattaunawa da dama da hukumomin UAE, gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa ‘yan kasar cewa nan ba da dadewa ba za a dage haramcin biza. A daidai wannan lokaci ne aka bayyana cewa Najeriya ta biya kashi 98 cikin 100 na dala miliyan 850 da ake bin kasar, lamarin da ke nuna an samu ci gaba wajen warware takaddamar dake tsakanin kasashen.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp