Wike zai gurfana gaban kwamitin ladabtarwa bisa zargin yi wa PDP zagon-kasa na "Anti Party"

 


Jam’iyyar PDP ta gayyaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, bisa zargin yi ma jam'iyyar zagon-kasa.

Mataimakin sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana haka a ranar Litinin a wani shiri na gidan Talabijin na Channels mai suna Sunrise Daily.

Abdullahi ya bayyana cewa an gayyaci Wike a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Tom Ikimi wanda kwamitin ayyuka na jam’iyyar ya kafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post