Wasu iyalai dake sansanin bayar da agaji a Maiduguri sun shiga rudani bisa umarnin gwamnati na mayar da su gidajen su

Wasu iyalai dake sansanin bayar da agaji a Maiduguri sun shiga rudani bisa umarnin gwamnati na mayar da su gidajen su

Matakin da gwamnatin jihar Borno ta dauka na rufe sansanonin bayar da agaji ga mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da gidajen su a Maiduguri Metropolitan Council da karamar hukumar Jere ya jefa wasu iyalai daga cikin su a cikin rudani


Wasu da suka tsira daga ambaliya da suka fake a cikin sansanonin sun ce matakin da gwamnatin jihar ta dauka zai jefa su cikin mawuyacin hali, saboda ba su da inda za su.


Sai dai tun bayan faruwar lamarin, jami’an gwamnati da wasu kungiyoyin agaji da ke kula da sansanonin, ke korafin cewa wasu mutanen da ambaliyar ruwan ba ta shafa ba, sun kutsa cikin sansanonin.


Mutanen da ke kusa da karamar hukumar Damboa da wasu daga cikin garuruwan Bama, Mafa, Dikwa da dai sauransu, sun yi zargin cewa sun koma sansanonin bayar da agajin gaggawa, duk a kokarinsu na karbar abinci da sauran kayayyakin tallafi da aka tanada domin wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a baya-bayan nan.


Kafa sansanonin wadanda ambaliyar ruwan ta shafa ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke kokarin ganin ta kammala tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su sama da shekara 15.


A halin da ake ciki, gwamna Babagana Umara Zulum ya ce sansanonin da ake gudanar da ayyukansu a makarantu ne kawai za a rufe domin ba da damar ci gaba da ayyukan koyo a fadin jihar baki daya.


Sai dai wakilin Daily Trust da ya zagaya birnin ya ga wasu daga cikin mutanen da suka bar daya daga cikin manyan sansanonin, wato Bakassi, da digo, kuma da yawa daga cikinsu sun ce jami’an sansanin sun sallame su. Sai dai wata mace mai suna Zara Isa da ta tsira daga garin Fari ta ce har yanzu ruwan yana kusa da gidajensu kuma ba ta san inda za ta dosa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp