Wani bangaren PDP na Katsina ya rantsar da sabbin shugabanni

Wani bangaren PDP na Katsina ya rantsar da sabbin shugabanni

Wani bangare na jam’iyyar PDP a jihar Katsina karkashin Sanata Yakubu Lado ya rantsar da sabon shugaban jam’iyyar, Alhaji Nura Amadi Kurfi tare da wasu abokan aikin sa.

An gudanar da bikin ne a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Katsina.

Alhaji Kurfi ya yabawa shugabancin jam’iyyar PDP na kasa da kuma Sanata Lado kan yadda jam’iyyar take cigaba da  samun nasara.


Ya bayyana abubuwan da ya mayar da hankali a kai da suka hada da hadin kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar, bin doka, da samar da daidaito a zaben 2027.


Wannan lamari dai na zuwa ne bayan da ake ta cece-kuce, yayin da wani bangare a karkashin jagorancin Mustapha Inuwa ya nemi zuwa kotu kan zargin fitar da mambobinsa daga tsarin.

Sai dai bangaren da Lado ya jagoranta sun gudanar da zabuka tun daga shiyya har zuwa jiha.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp