Sokoto na binciken karkatar da N16.1bn karkashin gwamnatin Tambuwal
Kwamitin bincike na jihar Sokoto na binciken sayar da hannayen jarin jihar na naira biliyan 16.1 da kamfanin jahar Sokoto ya yi a zamanin mulkin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Da yake zantawa da manema labarai, lauyan hukumar, Amanzi F Amanziz ya ce an bukaci hukumar da ta binciki zargin sayar da hannayen jarin jihar da kamfanin ya yi.
Yace a shekarar 2018, Akanta Janar ya mika dukkan hannayen jarin gwamnati ta hanyar wata wasika zuwa ga kamfanin zuba Jari na Jihar Sakkwato. Kuma a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023 an sayar da wadannan hannayen jari ba a san inda suke ba.
Don haka an yi kira ga hukumar da ta binciki yadda aka sayar da wadannan hannayen jari da kuma inda kudaden suke. Dangane da abin da ke cikin takardar, ana zargin jimillar Naira biliyan 16.1 da ba a san inda suke ba.