Shugaba Tinubu na aiki ba gajiyawa don tsaro ya inganta a Nijeriya - Kasshim Shettima

Mataimakin Shugaban kasa Sanata Kasshim Shettima ya ce shugaban kasar ba ya wasa da duk wani abu da ya danganci sha'anin tsaron Nijeriya.

Sanata Kasshim Shettima ya ce Shugaba Tinubu na aiki kan jiki, kan karfi don ganin tsaron lungu da sakon Nijeriya ya inganta ta yadda harkoki za su koma yadda ya kamata.

Da ya ke magana a fadar shugaban kasa, a lokacin da ya karbi bakuncin jagorancin kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN, Sanata Kasshim Shettima ya bukaci da a hada hannu waje daya don magance matsalolin tsaron da ake fama da su.

Mataimakin Shugaban kasar ya bukaci da a yi wa matsalar taron-dangi don ganin an magance ta cikin kankanin lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post