Shugaba Tinubu mai arziki ne, ya fi karfin ya wawuri dukiyar Nijeriya - A cewar Ministan Matasa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, mutum ne mai karfin arziki ba zai wawure dukiyar kasa ba, a cewar, karamin ministan ci gaban matasa Ayodele Olawande.

VON ta rawaito Olawande yana bayyana haka ne a taron mako na tattaunawa ta hadin gwiwa na ma’aikatar raya matasa ta tarayya a Abuja.


Ministan ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa nan da wani lokaci za a samu sauye-sauye masu kyau.


Yace ina rokon ku da ku yi hakuri da wannan gwamnati. Nan ba da dadewa ba Nijeriya za ta samu kyakykyawan tsari kuma rayuwar ‘yan kasar za ta sauya.


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba talaka ba ne, mutum ne da aka san yana da arziki, don haka ba za a ce masa yana son wawure dukiyar Nijeriya ba,kuma baya sha’awar wawure dukiyar kasar.

1 Comments

  1. Kai kuwa badai Dan asara ba, shugaba tunubu Yana wawasar kudin mune, tayadda Yana rasa yadda zaiyi dashi, Wanda ko gobara sukayi bazaiyi talauci ba, daga shi har iyalansa.
    Kai kuwa ba karamin Dan kutumar uba bane, Allah ya tsine maka Albarka Dede gwargwado

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp