Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Beijing na kasar Sin domin aiwatar da wasu ayyuka a kasar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Beijing na kasar Sin domin aiwatar da wasu ayyuka a kasar

Shugaban ya isa kasar Sin ne da sanyin safiyar Lahadinnan


A ranar Alhamis ne shugaban ya tashi daga Abuja zuwa babban birnin kasar Sin domin gudanar da wasu ayyuka a hukumance.


Mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale, ya ce shugaba Tinubu "zai yi dan takaitaccen aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa."


Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai, a fadar shugaban kasa, Ngelale ya ce, ana sa ran shugaban kasar zai shiga jerin tarurruka da "ayyukan da ke da amfani ga tattalin arzikin Najeriya da al'umma."


Ya ce, shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na kasar Sin, shugaba Xi Jinping, inda za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna kan hadin gwiwar, “tattalin arzikin, aikin gona, bunkasa fasahar tauraron dan adam, bunkasa sana'o'i, da inganta sana'o'i, gami da bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.


Wannan dai zai kasance wani bangare na tattaunawa mai zurfi inda shugabannin kasashen biyu za su tattauna batutuwan da suka shafi hadin gwiwa, ba wai kawai tattalin arziki ba, har ma da batun tsaron kasa,da kasa,.


Ngelale ya bayyana cewa, shugaba Tinubu zai kuma halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), inda shugabannin kasashen Afirka da dama za su halarci domin tattaunawa da shugabannin kasar Sin kan wasu muhimman batutuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post