Sama da mutum miliyan daya ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri – Zulum
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce adadin mutane miliyan 1 ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihar,da ta faru a ranar Talata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai, yayin da yake raba kudade da dafaffen abinci ga ‘yan gudun hijirar da suka fake a sansanin Bukassi,a Maiduguri.
Ya ce an kafa kwamitin bayar da agajin gaggawa na lafiya domin dakile annobar ambaliyar ruwa a Maiduguri da birnin Jere.
Ya ce ya zuwa yanzu, ba mu iya tantance yawan asarar da aka yi ba, amma kusan kashi daya bisa hudu na daukacin garin Maiduguri ya cika da ruwa.
Gwamnan ya ce mutanen da abin ya shafa sun kai miliyan 1, abin da muke yi a safiyar yau shi ne samar da agajin gaggawa, wanda ke da kyau da kuma bayar da abinci
Zulum ya bayyana cewa, tawagar bincike da ceto ta fara gudanar da ayyuka a fadin yankin al'ummomin da abin ya shafa domin tantance adadin asarar rayuka da dukiyoyi,za a tattara bayanan mutanen da abin ya shafa.
Gwamnan ya ce ya samu Naira biliyan 3 da aka ware don shawo kan ambaliyar ruwa daga Gwamnatin Tarayya kuma za a yi amfani da ita wajen magance kalubalen da ambaliyar ta shafa.
Hayatu Sade
ReplyDeletehayatusadesade@gmail.com
ReplyDelete