Jam’iyyar APC ta dage taron ta na kwamitin zartarwa da ta shirya yi a ranar 11 da 12 ga wannan Satumbar 2024.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Morka ya bayyana cewa nan gaba za'a sanar da ranakun taron lokacin da ya dace.
Jam'iyyar ta bayyana cewa an dauki matakin ne biyo bayan rashin shugaba Tinubu na halartar taron.