Kafin dakatar da shi, Sanata Tsauri na cikin kwamitin amintattu na jami'iyyar na kasa.
Sanarwar dakatarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jami'iyyar na mazabar Tsauri A. Danjume Abubakar da sakataren jami'iyyar Abdullahi Garba.
Sanarwar ta ce jiga-jigan jami'iyyar PDP na mazabar Tsauri A. cikin karamar hukumar Kurfi jihar Katsina na zargin Sanata Umar Tsauri da yi wa jami'iyyar zagon-kasa wato Anti-party da kuma furta wasu kalamai da suka ci kari da tsarin jami'iyyar.
Wannan dakatarwa dai na karkashin sashe na 59 (1) na kundin tsarin mulkin PDP da ya ba shugabannin jami'iyyar na mazaba ikon dakatar da duk wani mamba da ya saba doka.
DCL Hausa ta rawaito cewa Umar Ibrahim Tsauri dai ya zama Sanatan Katsina ta tsakiya daga shekarar 2003-2007 a karkashin jami'iyyar PDP. Sannan ya zama sakataren jami'iyyar PDP na kasa a shekarar 2017.