Nijeriya za ta zama jagorar kasuwar halal ta duniya mai jarin Dala bilyan Dubu 7 - Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Najeriya na kan gaba a fannin tattalin arziki ta bangaren Kasuwar Musulmi zalla da ake kira da Kasuwar halal ta duniya, wadda aka yi hasashen jarinta zai haura Dalar Amurka tiriliyan 7.7 a shekarar 2025

Kashim ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na tattalin arzikin Halal da aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja a yau Laraba, 18/09/24 

Mataimakin ya jaddada cewa girman tattalin arzikin Najeriya da yawan al'ummarta yana samar mata da damammaki musamman a bangaren bunkasa sashen saka hannun jari na halal.

Kasuwar Rumbun Halal wani shiri ne da ya kunshi sayar da ababen da addinin Musulunci ya halasta da suka hada da halatattun abinci da abin sha, da kayan kwalliya, da na gyaran jiki da yawon bude ido, har ma da takin zamani.

Mataimakin shugaban ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu saboda irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen tafiyar da tattalin arzikin na halal, musamman a fannin hada-hadar kudi, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen samar wa da halal muhalli a Najeriya 

Shettima, ya kuma jaddada bukatar jawo hankulan masu zuba hannun jarin kasashen duniya, da fadada harkokin kasuwanci a yankin, da kara wayar da kan jama'a domin bunkasa Halali a Najeriya

1 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp