Wata tawagar hadin gwiwar wasu ma'aikatun Nijar karkashin jagorancin sabon ministan mai, ta kai ziyarar aiki domin gani da ido na wurin da za'a gina sabon kamfanin matatar mai a cikin jihar Dosso.
Ana sa ran sabuwar matatar man za ta rika tace ganga dubu 30 a ko wace rana a tashin farko kafin daga bisani a fadada zuwa dubu 100 a kowace ranar.
Ko baya ga matatar man ma akwai kuma babban cibiyar samar da wutar lantarki a jihohin Tillaberi Dosso da babban birnin Yamai domin rage dogaro da na ketare inji hukumomin.