Mun sa a binciki dalilin tashin gobara a gidan gwamnati - Gwamnan Katsina Dikko



Gwamnan jihar Katsina ya kafa kwamitin da zai gaggauta bincikar dalilin tashin gobara a wani sashe na gidan gwamnatin jihar a Katsina.

Gobarar da ta tashi a sanyin safiyar Litinin, ta lalata karamin dakin taro (Mini Chamber) da ke kusa da ofishin Gwamnan jihar.

Sai dai jami'an kashe gobara na gwamnatin tarayya da na jiha sun yi kokari wajen dakile wutar kada ta bazu zuwa sassan gidan.

Kwamitin da aka kafa din ne ake kyautata zaton zai gano musabbabin tashin wannan gobara.

A cikin wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Yar'adua, daraktan yada labaran ofishin sakataren gwamnatin jihar ya sanya wa hannu, ta ce an dora wa kwamitin alhakin gano dalilin tashin gobarar da irin barnar da ta yi da sakacin da ya jawo tashinta da kuma ba da shawarwarin yadda za a magance afkuwar hakan a gaba.

'Ya'yan kwamitin sun hada da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Katsina, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri, kwamishinan kasafin kudi, kwamishinan shari'a, kwamishinan tsaron cikin gida da kwamishinan yada labarai da sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post