Matsalolin Nijeriya na bukatar a yi musu taron-dangi - Kasshim Shettima


Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kara jaddada bukatar hada karfi da karfe tsakanin gwamnati, da abokan huldarta, da sauran masu ruwa da tsaki don kawar da talauci da inganta rayuwa ga daukacin ‘yan Najeriya.

Shettima, ya fadi hakan ne a wajen taron majalisar tattalin arzikin kasa karo na 144 a Abuja, inda ya jaddada cewa, samar da yanayin da kowane dan Najeriya ke da damar ci gaba, abu ne da ke bukatar hadin kai.

Sanatan ya yaba da gudunmawar da masu ruwa da tsaki da suka hada da gidauniyar Bill & Melinda Gates da kuma rukunin kamfanonin Dangote suke bayarwa wajen gina ci gaban Najeriya a fannonin da suka shafi lafiya, abinci mai gina jiki, noma, da ilimi.

Taron na NEC ya kuma tattauna kan dabarun da za a bi don magance matsalar ambaliyar ruwa, da rashin abinci mai gina jiki, sannan da yadda za a samar da 'yan sandan jihohi, da maganin cutar shan inna, ciki kuwa har da bukatar a aiwatar da shawarwarin da aka amince da su a kwamitin wucin-gadi kan ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, fari da kwararowar Hamada, kana da kafa kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya, da kuma kawar da Cutar Polio).

Post a Comment

Previous Post Next Post