Matatar man Dangote za ta rika fitar da litar fetur milyan 25 duk rana


Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Nijeriya ta ce matatar man Dangote za ta rika samar da lita miliyan 25 ta man fetur duk rana a cikin watan Satumba.

Hukumar ta bayyana haka ne biyo bayan soma aikin tace mai da matatar Dangote ta soma.

Kazalika, an kuma kammala yarjejeniya da kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL na sayar da danyen mai ga matatar Dangote da kudin Naira.

Wannan ci gaban ya yi daidai da amincewar da majalisar zartaswa ta tarayya FEC ta yi na sayar da danyen mai ga matatar Dangote a kudin Naira tare da sayen man fetur daga matatar a cikin kudin gida.

A wani labarin kuma, Aliko Dangote, ya ce yarjejeniyar sayar da danyen man fetur ga matatar mansa a kudin Naira da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi zai rage matsin lamba da ake yi wa canjin kudaden waje da akalla kashi 40%.

Ya kuma nuna godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnatin sa bisa bullo da irin wannan dabarar.

Post a Comment

Previous Post Next Post