Manufofin Tinubu sun kara wahalhalu ga 'yan Nijeriya– APC

 Manufofin Tinubu sun kara wahalhalu ga 'yan Nijeriya– APC


Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bullo da shi sun kara wahalhalun tattalin arziki a Nijeriya.


Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa Barista Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin da yake mayar da martani ga tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma Salihu Mohammed Lukman.


Lukman dai ya zargi jam’iyyar APC da gazawa ga ‘yan Nijeriya, inda ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shugaban kasa mai ci Bola Ahmed Tinubu sun kasa cika alkawuran da suka dauka a yakin neman zabe.


Lukman ya kuma bukaci shugabannin ‘yan adawa da su hada kai su yi aiki tukuru don ganin bayan gwamnatin APC a zaben 2027.


Da yake mayar da martani, Morka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya bayar da hujjar cewa Shugaba Tinubu na daukar matakai masu tsauri don sake farfado da tattalin arzikin kasar da ya dade yana karyewa, yana mai bayanin cewa sauye-sauyen da ya yi sun kara wahalhalun tattalin arziki a kasar.


Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaba Tinubu tana daukar kwararan matakai don sake farfado da tattalin arzikin kasar, da inganta tsaron kasa da kuma maido da kasar nan zuwa ga ci gaba mai dorewa.


Ya ce wadannan sauye-sauyen da babu makawa sun kara wa al’ummarmu wahalhalun tattalin arziki. Hasali ma rashin son gwamnatocin da suka gabata na yin wadannan gyare-gyare da magance matsalolin da suka samo asali ne ya sa tattalin arzikin kasar ya dade yana cikin tabarbarewa.



Amma bisa sabon tsarin fatan gwamnatinsa, ya zabi ya magance matsalolin tattalin arzikin kasar nan domin amfanin ‘yan Nijeriya baki daya.



Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp