Majalisar dokokin Kano ta amince da kasafin kudin cike gibi N99.2bn da gwamnatin jihar ta aike mata
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kasafin kudin cike gibi na naira biliyan 99.2 ta da gwamnatin jihar ta aike mata akwanakin baya.
An amince da kasafin kudin cike gibin ne bayan majalisar ta yi zama na Uku a yau alhamis
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin cike gibin a ranar 26 ga Agusta, 2024 inda ya nemi a kara kasafin kudin zuwa N536, 559, 816, 357.84 daga farkon N437, 338, 312, 787 da aka sanya wa hannu a watan Disamba 2023.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Hon Aminu Sa’ad, ya bayyana cewa kashi 58% na kasafin kudin an ware su ne domin a cigaba da yiwa al'umma aikin raya kasa.
Hon Sa’ad ya kara da cewa karin kasafin kudin zai kunshi zabukan kananan hukumomi da ke tafe, da biyan sabon mafi karancin albashi, da kudin gudanar da aiki a sabbin ma’aikatun da aka kafa da sake bude cibiyoyin koyar da sana’o’i da sauran ayyukan da gwamnati ta sa gaba.
Hakazalika, Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gina dakunan kwanan dalibai domin samar da ingantattun masauki ga daliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.