Kungiyar likitoci a Nijeriya ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da ta shiga a ƙasar.
Kungiyar ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin 26 ga watan Agusta saboda sace wani dan kungiyar mai suna Dokta Ganiyat Popoola-Olawale.
Kungiyar ta ce ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin jawo hankalin masu ruwa da tsaki don ganin an sako dan kungiyar da aka sace cikin gaggawa.
Category
Labarai