Kwalara ta halaka mutane bakwai, 71 suna kwance a asibiti a Adamawa
Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar kwalara a karamar hukumar Yola ta Arewa da ke jihar Adamawa, yayin da wasu 71 ke kwance a asibiti.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta raba a shafinta na X a ranar Talata.
A cewar NEMA, barkewar cutar amai da gudawa ta samo asali ne sakamakon ambaliyar ruwa da ta gurbace al’ummar yankin,Alkalawa, Doubeli, Rumde, da Gwadabawa.
Sanarwar ta kara da cewa kimanin mutane 100 ne kuma ake sanya ido a kai.
Ya zuwa ranar 16 ga Satumba, 2024, an kwantar da marasa lafiya 71 a asibiti, sama da 100 kuma ana duba lafiyarsu, kuma bakwai an tabbatar da mutuwarsu.