Kungiyar kwadago ta kasa NLC shiga wata ganawar sirri kan tsare shugaban ta Ajaero
Bayan tsare shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya Joe Ajaero da DSS ta yi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Burtaniya domin halartar taron ma'aikatan duniya, kungiyar NLC ta shiga wani taron sirri.
Shugaban hulda da jama’a na NLC, Benson Upah ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya fitar.
A cewar Upah, jami’an gwamnatin Nijeriya sun kama Ajaero ba tare da wani sammaci na doka ba, kuma ba a san inda yake ba da kuma halin lafiyarsa a halin yanzu.
Kungiyar ta NLC ta yi Allah wadai da tsarewar ashugaban nata ta ce wannan "aiki ne na rashin bin doka da kuma tsoratarwa" tare da neman a gaggauta sakin Ajaero ba tare da wani sharadi ba.
Majalisar ta kuma yi kira ga kasashen duniya, kungiyoyin kare hakkin dan Adam, da masu rajin tabbatar da dimokuradiyya da su lura da yadda ake samun karuwar mulkin kama-karya a Nijeriya.
An shirya Ajaero zai yi jawabi a taron da zai je a Burtaniya a madadin ma’aikatan Nijeriya, inda zai tattauna muhimman batutuwa kamar ‘yancin ma’aikata, adalcin zamantakewa, da daidaiton tattalin arziki.
A halin yanzu dai Majalisar na yin wani zama na sirri domin tattauna lamarin, kuma nan ba da jimawa ba za a bayyana sakamakon da aka samu a bainar jama'a."