Kungiyar Kwadago ta kasa NLC da wasu sauran kungiyoyi sun bukaci a sauya farashin man fetur daga yadda yake yanzu
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC ta bukaci da a gaggauta cire karin farashin man fetur na da akayi a kwanakin nan a fadin kasar.
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya ce kungiyar kwadagon na ganin gwamnatin tarayya ta ci amanar su kan sabon karin farashin man fetur.
Duk da cewa kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) bai sanar da karin farashin a hukumance ba, amma gidajen man da sauran manyan gidajen mai a fadin kasar sun daidaita farashin man fetur a ranar litinin.
A Legas, tashoshin NNPC sun maida farashin su zuwa N855 daga N568; Kano, N902; Abuja, N887 akan kowace lita daga N617.
Hakan ya faru ne kwanaki biyu bayan da hukumar NNPCPL ta sanar da jama’a bashin dala biliyan 6 da ta ke bin masu shigo da kaya da kuma matsalolin kudi da take fuskanta.
Ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa kungiyar kwadagon, a lokacin da ake tattaunawa kan mafi karancin albashin su zabi wani kaso a kara farashin man fetur ko kuma su karbi Naira 70,000 a mafi karancin albashi sannan a bar farashin man fetur ya ci gaba da zama kamar yadda yake.
Amma, bayan wata daya da gwamnati har yanzu ba ta fara biyan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ba, sun fuskanci abubuwan da ba za su iya bayyanawa ba.