Kungiyar Dalibai ta kasa sun yi barazanar rufe manyan biranen Nijeriya

Kungiyar Dalibai ta kasa sun yi barazanar rufe manyan biranen Nijeriya



Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta sanar da shirin ta na rufe dukkan manyan biranen Nijeriya daga ranar 15 ga Satumba, 2024.wannan na a wani mataki na martani ga karin farashin man fetur da aka yi a kwanakin nan.


A ranar Talata ne dai aka samu karin farashin man fetur kimanin ₦887 kan kowace lita, kuma an aiwatar da hakan a duk gidajen mai na NNPC.


Hakan ya haifar da cece kuce a duk faɗin ƙasar tare da ƙungiyoyin ma'aikata suna neman a sauya sabon farashin nan take.


A wata sanarwa da ya fitar ranar Larabar nan Okunomo Henry Adewumi, shugaban dattawa ta NANS, ya bukaci a gaggauta sauya farashin man fetur.


Sanarwar ta ce za a gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana da bin doka.


Yace sun rubuta ne domin sanar wa game da rufe dukkan manyan biranen Nijeriya, daga ranar 15 ga Satumba, 2024, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi.


Karin farashin man fetur da aka yi a baya ya kawo wa talaka wahalhalu, kuma ba za mu iya tsayawa muna kallo ba alhalin muna ganin makomarmu.



Muna kira ga daukacin daliban Nijeriya a fadin kasar nan da su amsa wannan kira, domin za mu mamaye dukkan manyan biranen kasar a ranar 15 ga Satumba, 2024. Ba za mu yi shiru ba, kuma ba za a tsorata mu ba. Za mu tashi tare domin neman ingantacciyar Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post