Ku rage farashin man fetur, ‘yan Nijeriya na fama da yunwa, Kukah ya fadawa jam;iyyar APC
Babban limamin cocin Katolika na Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya bukaci shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da su rage farashin man fetur a halin yanzu, yana mai cewa ‘yan Nijeriya na fama da yunwa.
Ya yi wannan jawabi ne a Juma’ar nan a Abuja, yayin da ake kaddamar da cibiyar ci gaba (TPI).
A ranar Talatar da ta gabata ne farashin man fetur a Nigeriya ya karu daga N855, zuwa N918,a gidajen man 'yan kasuwa kuwa ana sayar da man N1000,zuwa 1200 a cikin kasar.
Kukah ya ce,‘yan Nijeriya jin yunwa, ya kamata a nemo hanyar rage farashin man fetur a wannan lokaci.
Ya ce mu tuna da cewa idan har ba a kafa dimokuradiyya a kan ingantaccen tushe ba, to za mu yi gini a kan yashi, don haka ya kamata mu gyara matsalar dimokradiyya a Nijeriya.