Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta sa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku da tsohon babban sakataren ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu Bello Yero a gidan yari bisa zargin laifukan cin hanci da rashawa.
An kama mutanen biyu ne a ranar 27 ga watan Satumba, bisa zargin karkatar da kudi N27bn mallakar ma'aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu.
Sai dai, bayan gurfanar da su gaban kotu, wadanda ake tuhumar, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, ta ce ba su amsa laifin da hukumar ke tuhumarsu ba kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.