Kashim Shettima ya gayyaci Lokpobiri, Kyari zuwa villa kan karin farashin man fetur
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya gayyaci karamin ministan albarkatun Man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, zuwa Aso Rock.
Shi ma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya halarci taron wanda hakan bai rasa nasaba da karin farashin mai.
Haka kuma a taron akwai wasu jami’an gwamnati daga ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Karin farashin man fetur na baya-bayan nan ya sa farashin sufuri ya tashi sama da kashi 50 a manyan biranen Nijeriya.
Sabon karin farashin, wanda Kamfanin (NNPCL) ya aiwatar, ya tashi daga N855 zuwa N897 kowace lita, ya danganta da wurin da ake ciki, daga N568-N617 a baya.
‘Yan kasuwa masu zaman kansu sun maida farashin su zuwa tsakanin N930 zuwa N1,200 kowace litar man fetur.